Jam’iyyar NNPP ba ta da kudin kalubalar Nasarar Tinibu a kotu – Buba Galadima.
Jigo a jam’iyyar NNPP Buba Galadima ya bayyana cewa, NNPP taki kalubalantar nasarar da zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya samu a zaben shugaban kasa na 2023 a gaban kotu ne, domin ba ta da kudin da za ta yi hakan.
Galadima ya sanar da hakan ne a hirarsa da gidan talabijin na ARISE a kan ganawar sirri da tsakanin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na NNPP da Tinubu a kasar Faransa.
An ruwaito cewa, Tinubu ya yi ganawar sirrin ne da Kwakwaso don ya samar da masahala a tsakanin Kwankwaso da Abdulmumin Jibrin, tsohon jami’in yakin neman zaben Tinubu kuma zababben dan majalisar wakilai da ya sauya sheka zuwa NNPP daga APC kafin zaben 2023.
Sai dai, ba a samun cikakkun bayanai kan ganawar sirrin da Tinubu ya yi da Kwankwaso ba, amma an ce, sun tattauna kan kafa gwamnatin hadin kan kasa a tsakanin jami’iyyun biyu.
Galadima da yake mayar da martani kan ganawar sirrin ta manyan ‘yan siyasar biyu ya ce, babu wani labari domin abu ne da bisa tahirin siyasar Nijeriya, hakan ya saba farauwa.
Ya ci gaba da cewa, komai yau a Nijeriya ya na zama labarai, inda ya ce, ganawar a tsakanin jagororin ‘yan siyasar biyu, bai kamata ace ta ja hankalin mutane ba.
Ya ci gaba da cewa, kamar yadda ku ka sani ne, Kwankwaso ya yi takarar shugaban kasa da Tinubu a 2023, inda NNPP ta zo na hudu, inda ya sanar da cewa, NNPP ce kawai ba ta je kotu ba, wanda mune ke da cikakkun dalilan zuwa kotu.
A cewarsa, ganawar sirri irin wannan da kuma tunanin kafa gwmnatin hada kan kasa, ba sabon abu ne a harkar siyasar Nijeriya ba domin irin wannan, ta taba faruwa a jamhuriya ta farko a tsakanin jami’yyun NCNC da NPC a tsakanin jam’iyyun Azikiwe da Ahmadu Bello.
Ya bayyana cewa, daga baya sun kafa gwmnatin hada kan kasa a tsakanin NPC da NNDP wadda Cif Samuel Akintola na gabas ya jagoranta.
Ya kara da cewa, har ila yau, a rubuce yake a lokacin gwamnatin Shagari, jami’yyar NPP da Nnamdi Azikiwe ke jagoranta, sun kulla yarjejeniya da gwmnatin NPN.
Galadima ya yi nuni da cewa, wannan tarihi ne ya sake mai-maita kansa, a saboda haka ya na da kyau a ilimantar da matasa kan tarihin kasar su.
Da yake mayar da martani kan abinda yasa NNPP ba ta kalubalanci nasarar Tinubu a kotu kamar yadda PDP da LP da sauran jami’iyyu suka yi, ba Galadima ya ce, NNPP ba ta da wadatattun kudin da za ta yi hakan.
Ya ce, wannan abun a rubuce yake cewa, PDP ce ta kore mu ni da Kwankwaso, ba wai mun shiga takarar don mu dakatar da su daga cin nasara a zaben bane.
Ya ce, muna sane da cewa, zuwa kotu na bukatar kudade masu yawa wanda bamu da su, inda ya ce, duk wanda zai je kotu don kalubalantar zabe, akalla sai ya tanadi Naira biliyan biyar, mu kuma, ba mu da wadannan kudaden.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.